A ranar 20 ga watan Yulin bana, an gano gawarwaki 85 a gefen buhunan abinci masu dauke da tambarin MDD, wadanda suka hada da mata da yara. Wasu na ci gaba da rike buhunan abinci lokacin da aka same su, yayin da wasu yaran ke cikin yanayi na nuna galabaita kafin mutuwarsu.
Wannan shi ne mummunan sakamakon harin sama da Isra’ila ta kai a wani wurin rarraba kayan agaji a zirin Gaza. Abun takaici shi ne, ba wannan ne karon farko da aka samu irin wannan abun ba. Wani rahoton MDD ya nuna cewa, mutum guda na mutuwa a duk minti uku a fagen yaki a fadin duniya. Mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon yaki, su ne mafi daukar hankali a cikin alakar zaman lafiya da ci gaba.
Yayin da ake rasa zaman lafiya, rayuwar dan Adam na zama mai matukar wahala, balle ma batun samar da ci gaba. Lokacin da ake cika shekaru 80 da samun nasarar yakin duniya na biyu a halin yanzu, manufar samar da ci gaba cikin lumana ta kasar Sin, ta amsa tambaya game da tsarin kiyaye zaman lafiya da samun ci gaba tare, bisa wayewar kanta mai zurfi, da hanyar samun ci gaba mai amfani, da kuma ra’ayinta na kula da kasa da kasa. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp