A ranar 5 ga wata agogon Amurka, shugaban kasar Donald Trump ya rattaba hannu kan wata doka ta zartaswa don maido da sunan tarihi na ma’aikatar tsaron Amurka, inda ya sake mata suna zuwa “ma’aikatar yaki”. Dokar zartaswar ta bayyana cewa, wannan matakin na da nufin aike wa da abokan takun-saka ne cewa, Amurka a shirye take ta shiga yaki domin kare muradunta.
Wata kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar tsawon shekaru biyu a jere daga shekarar 2023 zuwa ta 2024 tsakanin mutane 14,071 da suka fito daga kasashe 38 na duniya ta nuna cewa, dabi’ar amfani da karfin soja ta yi mummunar zubar da kimar Amurka a duniya, kuma masu bayyana ra’ayoyin gaba daya suna tambaya game da sahihancin zaman Amurka “jagora” a huldar kasa da kasa.
A cikin binciken, kashi 61.3 cikin dari na masu bayyana ra’ayoyin sun yi imanin cewa, Amurka ce ta fi kowace kasa fama da yaki a duniya. Kashi 70.1 cikin dari kuma sun yi imanin cewa, yakin da Amurka ke afkawa a kasashen waje ya haifar da mummunar matsala ga rayuwar bil’adama a duniya. Masu bayyana ra’ayoyin daga kasashen Turai da kudancin Amurka sun fi nuna ra’ayin hakan ma, inda kasonsu ya kai 74.3 da kuma kaso 77.4 bi-da-bi.
Wani kaso 73.9 cikin dari na masu bayyana ra’ayoyin kuma daga kasashen Turai sun ce, yawan taimakon soji da Amurka ke ba wa wasu kasashe yana barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Har ila yau, kaso 57.4 cikin dari na masu bayyana ra’ayoyin kuma sun yi imanin cewa, kungiyar tsaro ta NATO da Amurka ke jagoranta ta ta’azzara zaman dar-dar a matakin yankuna na duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp