Yayin wani faretin soji a birnin Beijing, makamai masu linzami rundunar sojin China ta People’s Liberation Army na wucewa a hankali rataye a kan manyan motoci masu launin kakin soji.
Makaman masu tsawon mita 11 da nauyin tan 15, kowannensu na dauke da kalmomi da lambobi na “DF-17”.
- Chelsea Ta Kammala Ɗaukar Jamie Gittens Daga Borussia Dortmund
- Xi Ya Gana Da Shugaban Jam’iyyar United Russia
A wannan lokacin ne China ta kaddamar wa duniya da sabon makaminta Dongfeng mai linzami mai gudun walkiya wanda ake kira hypersonic a Turance.
An yi hakan ne ranar 1 ga watan Oktoban 2019.
Da ma Amurka na sane da shirin na China, amma kuma tuni Chinar ta ci gaba da inganta makaman tun daga lokacin.
Saboda tsabar gudunsu da kuma zilliya inda suke da sauri ninki biyar na gudun sauti makamai ne da ka iya sauya yadda ake fafata yaki a yanzu.
Hakan ta sa yanzu kasashe ke rige-rigen samar da su.
Rasha, China, Amurka: rigegeniyar nuna iko Bikin faretin na Beijing ya jawo rade-radi game da barazanar da China ke yi wa kasashen Yamma da makamanta masu linzami. Yanzu ita ce kan gaba wajen samar da su, sai kuma Rasha da ke biye mata.
Amurka kuma, na kokarin kamo su ne, yayin da Birtaniya kuma ba ta da su.
William Freer, wani mai nazarin harkokin tsaro a cibiyar Council on Geostrategy, na ganin dalilin da ya sa Rasha da China suka zarce saura abu ne mai sauki.
“Sun yanke shawarar zuba kudade masu yawa a wadannan fannonin tun shekaru baya.”
A gefe guda kuma, kasashen Yamma sun fi mayar da hankali tun daga shekara 20 da suka wuce wajen yaki da masu ikirarin jihadi a gida da kuma kasashen waje.
A lokacin, yiwuwar gwabza yaki tsakanin manyan kasashe masu karfin soji iri daya ba ta da yawa.
Aikin gwajin wani makami mai linzami mai matsakaicin nisa a Koriya ta Arewa
“Abin da ya faru shi ne, mun gaza wajen lura da barazanar China wajen inganta rundunar sojinta,” kamar yadda Sir Aled Younger, wanda ya bar mukamin shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta Birtaniya a 2020, ya bayyana.
Sauran kasashe na ta kokari su ma: Isra’ila na da makamin hypersonic mai suna Arrow 3 wanda aka kirkira domin kakkabo makamai.
Iran ta yi ikirarin cewa tana da shi, wanda ta ce ta harba wa Isra’ila lokacin yakin kwana 12 da suka gwabza a watan Yuni.
(Tabbas makamin ya yi gudun walkiya amma ba a tunanin yana da ikon zilliya mai yawa da za a kira shi cikakken hypersonic).
Koriya ta Arewa ma na ta yin aiki kan nata tun 2021, har ma ta yi ikirarin cewa tana da makamin.
Yanzu Amurka da Birtaniya na zuba kudade a fannin makaman hypersonic, kamar yadda saura kamar Japan da Faransa ke yi.
Amurka ta kaddamar da nata makamin mai gudun hypersonic mai suna “Dark Eagle”.
Amma dai a yanzu China da Rasha ne kan gaba sosai, inda wasu masana a kasashen Yamma ke cewa abin damuwa ne.
Dankaren gudu da mummunar barna
Kalmar hypersonic na nufin wani abu mai gudun tsiya kan ma’aunin March 5 ko sama da haka. Ma’ana mai gudu ninki biyar na sauti ko kuma gudun mil 3,858 cikin awa daya.
Wannan gudun nasu shi ne abin da ya sa ake fargaba game da su.
Makamin da aka sani mafi gudu zuwa yanzu shi ne na Rasha mai suna Abangard – wanda aka ce ya kan yi gudun Mach 27 (kusan mil 20,700 cikin awa daya), kodayake an fi ambato gudun Mach 12.
Game da barnar da suke haifarwa, irin wadannan makaman ba su fi sauran makamai masu linzami hadari mai yawa ba, a cewar Mista Freer.
“Wahalar ganowa da kuma kakkabo su ce ke sakawa ana tsoronsu sosai.”
Akan harba su ne da taimakon wata roka, idan suka kai kololuwar tashi sai kuma su shiga wani yanayi da ake kira “scramjet engine” wanda shi kuma zai yi musu jagora domin dira inda aka aika su.
Akan yi amfani da su ta hanya biyu, ma’ana bam din suke dauke da shi zai iya zama na nukiliya ko kuma gama-garin bam.
Kafin a ayyana makami a matsayin mai gudun walkiya na hypersonic, dole ne sai ya mallaki ikon zillewa makaman kariya. Wanda ya harba shi zai dinga sassauya masa hanyar tafiya ta yadda abokin gabarsa ba zai iya gane shi ba har sai ya dira kan wurin da ya nufa.
“Ta hanyar kauce wa nau’rorin leken samaniya, sukan kauce wa abokan gaba har sai lokacin da suke dab da isa wanda hakan zai sa babu damar da za a iya tare su,” Patrycja Bazylczyk, mai bincike a sashen Missile Defence Project na cibiyar Centre for Strategic and International Studies da ke Amurka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp