Kamfanin Aero Engine Corporation na kasar Sin, ya fitar da sabon injin aiki a manyan na’urori mai aiki da iskar gas mai karfin gaske, wanda ke iya samar da karfin megawatt 110.
Kamfanin ya fayyace sashen kirar injin mai suna Taihang 110, a yankin kira na kamfanin a Litinin din nan, kuma ana fatan fara shigar da injin kasuwa.
Fitar da injin zuwa kasuwanni na nufin kasar Sin ta cimma nasarar gabatar da inji kirar gida mai matukar karfi, wanda manyan na’urori za su rika amfani da shi ta hanyar sarrafa iskar gas. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp