Ministar shari’a ta kasar Sin He Rong, ta ce kasar Sin ta zama wurin da aka fi zaba na warware takkadamar cinikayya da ta shafi kasa da kasa, tana mai bada misali da karuwar adadin irin wadannan batutuwa cikin shekaru 5 da suka gabata.
Yayin wani taron manema labarai a yau, He Rong ta ce an warware sama da takkadama 16,000 dake da alaka da kasashen waje, da suka shafi jimilar kudi yuan biliyan 730 (kimanin dala biliyan 102.8) a kasar, a lokacin.
Ta kara da cewa, a shekarar 2024 kadai, kasar ta karbi irin wadannan batutuwa sama da 4,400, wadanda suka shafi kusan yuan biliyan 200. Idan aka kwatanta da shekarar 2020, adadin batutuwan ya karu da kaso 100, na jimilar kudi kuma ta karu da kaso 136.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp