A yau Litinin, wasu rahotanni na cewa, yayin wani taron manema labaru na musamman kan zuba jari ga sassan ketare da aka gudanar a taron tattauna harkokin cinikayya da zuba jari na kasa da kasa na Sin karo na 25, cewa a shekarar 2024 adadin jarin da kasar Sin ta zuba kai tsaye a kasashen da suka shiga shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ya kai dalar Amurka biliyan 50.99, adadin da ya karu da kashi 22.9 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar 2023.
A dai yau din, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin, da hukumar kididdiga ta kasar, da hukumar kula da musayar kudin waje ta kasar, sun fitar da sanarwar “kididdiga ta shekarar 2024 kan zuba jari kai tsaye da kasar Sin ta yi ga kasashen ketare”.
Sanarwar ta nuna cewa, a karshen shekarar 2024, masu zuba jari na kasar Sin sun kafa masana’antu dubu 52 a kasashe da yankuna 190 na duniya, kuma dubu 19 daga cikin adadin, an kafa su ne a kasashen da suka shiga shawarar Ziri Daya da Hanya Daya. (Safiyah Ma)
 
			




 
							








