A ranar Litinin ne gwamnatin tarayya ta shiga wata muhimmiyar tattaunawa da shugabannin kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta kasa (NUPENG) da shugabannin gudanarwar matatar man Dangote a wani gagarumin yunkuri na warware yajin aikin da kungiyar ke ci gaba da yi wanda ya kawo cikas ga rarraba man fetur a fadin kasar nan.
Taron wanda aka kira a hedikwatar ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi da ke Abuja, ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Muhammad Maigari Dingyadi ne ke jagoranta.
- Abin Fargaba Ne Yadda Bashin Nijeriya Ya Haura Tiriliyan 149 – Shugaban Majalisar Wakilai
- Adadin Kamfanonin AI A Sin Sun Haura 5,000
Duk da cewa, an shirya fara taron ne da misalin karfe 10 na safiyar ranar Litinin, amma tawagar ta NUPENG ba ta isa wurin da wuri ba har sai misalin karfe 5:05 na yamma, lamarin da ya sa aka fara muhimmin taron a makare.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da jami’an Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), wakilan kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, shuwagabannin kamfanin ‘MRS Holdings Limited’ da kuma kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa (TUC).
Da yake bayyana bude taron, Minista Dingyadi ya jaddada aniyar gwamnati na sulhu a tsakanin kungiyar da masu gudanar da masana’antu. Ya bayyana bangaren mai da iskar gas a matsayin jigon tattalin arzikin Nijeriya, yana mai gargadin cewa tsawaita yajin aikin zai haifar da mummunan sakamako ga kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp