Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta yi Allah-wadai da wani harin da ‘yan ta’adda suka kai a garin Darul Jamal, dake yankin Bama na Jihar Borno.
Mista Mohamed Malick Fall, Babban Jami’i mai Kula da Ayyukan Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya, ya bayyana matukar bakin cikinsa kan lamarin, wanda ya faru a yammacin ranar 5 ga watan Satumba.
- Neman Gurbi: Nijeriya Za Ta Kece Raini Da Afirka Ta Kudu A Bloemfontein
- Sojoji Sun Kai Hare-hare 261, ‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 1,950 A Watan Agusta – NOA
“Ina matukar bakin ciki da rahoton kisan da aka yi wa sojoji da fararen hula da dama a ranar Juma’a a kauyen Darajamal da ke Karamar Hukumar Bama, a Jihar Borno a arewa maso gabashin Nijeriya,” in ji Fall.
“Bai kamata fararen hula su zama abin kai wa hari ba”.
Rahotannin farko sun nuna cewa an kashe fararen hula fiye da 50, inda ake zargin an yi garkuwa da wadanda ba a san adadinsu ba. Wasu da dama sun gudu, kuma gidaje fiye da 20 sun kone kurmus a lokacin harin. Adadin wadanda suka jikkata na iya karuwa yayin da ake samun karin bayanai.
A madadin MDD a Nijeriya, Fall ya mika ta’aziyya ga iyalan wadanda kai harin ya shafa, gwamnati, da kuma al’ummar Jihar Borno, tare da yi wa wadanda suka ji rauni fatan samun sauki cikin gaggawa.
“Ina kira ga hukumomin tsaro da su kamo wadanda suka kai wannan danyen aikin. Ina kuma kira da a gaggauta sakin duk wadanda aka sace,” in ji shi.
Jami’in MDD ya bayyana lamarin a matsayin wani mummunan tunatarwa kan yadda tashe-tashen hankula da rashin tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a Jihar Borno a duk shekara.
Rahotanni sun nuna cewa an dade ana kashe fararen hula, ‘yan gudun hijira (IDP), manoma, matafiya, da ‘yan kasuwa a irin wadannan hare-haren. Dabarun da Yan ta’adda ke amfani da su sun hada da bama-bamai, da kai harin kunar bakin wake, da dai sauran munanan hanyoyi.
“Ina kira ga bangarorin da ke rikici da su kare fararen hula da dukiyoyinsu da kuma bin dokokin ayyukan jin kai na duniya da kare hakkin dan’Adam,” in ji shi.
MDD ta sake jaddada aniyar ta na ci gaba da tallafa wa wadanda rikici ya shafa a Nijeriya, a kokarin da gwamnatin ke yi na kara mayar da martanni.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp