Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, ta cika kashi 80 cikin 100 na bukatun kungiyar malaman Jami’oin kasar nan, ASUU.
Gwamnatin na mayar da martani ne kan matakin da kungiyar ASUU ta dauka na kara wa’adin watanni shida na yajin aikin da take yi.
Daraktan sashen yada labarai na ma’aikatar ilimi ta kasa, Bem Gong a martanin da ya mayar ya kafe cewa, Gwamnatin ta dauki dukkan matakan da suka kamata domin a kawo karshen yajin aikin kungiyar, “Gwamnati ta cika kashi 80 Cikin 100 da kungiyar ta bukata, don haka babu kuma wata bukatar cigaba da yajin aikin.”
ASUU dai, tun a watan Fabrairun 2022 ne ta tsunduma cikin yajin aiki a kan bukatun da take nema a biyata na yarjejeniyarsu da Gwamnatin Tarayya a shekarar 2009.