Rundunar ‘yansandan jihar Katsina ta kama wani matashi dan shekaru 38 da haihuwa bisa zargin mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba da kuma yin sojan gona.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu wanda ya bayyana haka, ya bayyana wanda ake zargin a matsayin Mubarak Bello da ke unguwar Kofar Yamma a karamar hukumar Kurfi.
Aliyu ya ce an kama Bello ne a wani sintiri na yau da kullum da misalin karfe 2:30 na safe. a ranar 13 ga Satumba.
A cewar kakakin ‘yansandan, jami’an sun tare wata mota kirar Toyota Corolla mai launin toka mai lamba GGE 473 BH bayan direban ya kasa bayar da kwakkwaran bayanin kansa da kuma motar.
Ya bayyana cewa binciken da aka yi wa motar ya kai ga gano wata bindiga da aka kera a cikin gida, harsashi masu rai guda hudu, fasfon aikin ɗansanda na bogi da kuma waya lambar mota mai lamba FGE 68 a Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp