Rahotanni daga ƙaramar hukumar Dandi a Jihar Kebbi, sun tabbatar da cewa wasu ‘yan ta’addan Lakurawa sun kai hari garin Filgila, inda suka kashe jami’in kwastan mai suna Sani Shuaibu.
Sani Shuaibu, wanda dan asalin Jihar Yobe ne, yana aiki ne a sashen Federal Operations Unit (FOU) mai hedikwata a Kaduna.
- Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 11 A Borno Da Adamawa
- Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi
Shaidu sun ce lokacin da abin ya faru, marigayin yana zaune ne a masallacin sansaninsu.
Lakurawan sun fara kai hari cikin gonakin manoma, daga nan kuma suka doshi wajen jami’an Kwastam.
An ce sun fara harbi, amma Sani ya yi ƙoƙarin tserewa cikin gonar masara kafin harsashi ya same shi.
An garzaya da shi zuwa babban Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Kebbi, inda daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
An yi jana’izarsa a babban masallacin Sarkin Gwandu, sannan aka binne shi a makabartar Dukku da ke kan hanyar Makera zuwa Kangiwa.
Jana’izar ta samu halartar jami’an kwas5tan, ‘yan uwa, abokai da sauran mu5sulmi daga sassa daban-daban na jihar.
Har yanzu al’ummar garin Filgila da kewaye na cikin tashin hankali da fargaba, kasancewar hare-haren Lakurawa na jefa su cikin zulumi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp