’Yansanda a Jihar Jigawa sun kama wani mutum da ya sanye da kakin soja tare da wasu mutum uku da ake zargi da satar motoci.
Kakakin rundunar ’yansandan jihar, SP Shiisu Lawan Adam ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Laraba.
- Ya Kamata A Kiyaye Nasarorin Da Aka Cimma A Shawarwarin Sin Da Amurka
- Manyan Ma’aikatan FIRS 4 Sun Rasu Sakamakon Gobarar Da Ta Tashi A Ginin Afriland A Legas
Ya bayyana cewa an kama su ne a ranar Talata da misalin ƙarfe 7:50 na safe.
Sun yi hatsari da wata mota da suka sato a ƙauyen Sabon Sara da ke Ƙaramar Hukumar Kafin Hausa.
Duk da sun yi ƙoƙarin tserewa, ’yansanda suka cafke su.
Tun a ranar 7 ga watan Satumba, 2025, wani mutum mai suna Hussaini Manager ya kai rahoto ofishin ’yansanda na Kafin Hausa cewa an sace masa mota ƙirar Golf mai launin shuɗi mai lambar MGA 108 JG a Agura Motor Park, Kafin Hausa.
Bincike ya gano cewa ɗaya daga cikin mutanen na yin sojan gona ne, yana kiran kansa Lance Corporal Kabiru Musa, alhali kuma ɗan asalin unguwar Rimin Kebe ne a Jihar Kano.
Lokacin da aka cafke su, an samu mota, katin ATM guda bakwai, lasisin tuƙi guda biyu, da wasu abubuwa da ake zargin na damfara ne a hannunsu.
Bayan kammala bincike, an gurfanar da su a gaban kotu.
Kwamishinan ’yansandan Jihar Jigawa, Dahiru Muhammad, ya yaba wa jami’an Kafin Hausa bisa ƙwazo da ƙwarewar da suka nuna wajen cafke mutanen.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp