Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana ra’ayin kasar Sin game da rikicin da ake yi yanzu haka tsakanin Falasdinu da Isra’ila a ranar Jumma’a 19 ga wata, yayin wata tattaunawa da ministan harkokin wajen kasar Morocco Nasser Bourita a birnin Beijing.
Yayin da yake nuni da cewa, ya kamata kasashen duniya su hada kai wajen tunkarar halin gaggawa da ake ciki a yanzu, Wang ya ce, ya zama wajibi a karfafa tsagaita bude wuta a zirin Gaza tare da daukar matakin gaggawa don magance bala’in tabarbarewar jin kai da ake fuskanta a halin yanzu.
Wang ya ce, dole ne a aiwatar da ka’idar bar “Falasdinawa su mulki Falasdinu” a kan turbar gaskiya. Kuma Gaza da yammacin gabar kogin Jordan duk yankuna ne na Falasdinu da ba za a iya raba su ba. Sannan ya kamata duk wani tsarin shugabanci da na sake gina yankin bayan yaki ya mutunta ra’ayin al’ummar Falasdinu tare da kare halastattun hakkokin kasar Falasdinu.
Wang ya kuma jaddada wajibcin tsayawa tsayin daka kan shawarar kafa kasashe biyu masu cin gashin kansu, da kara cimma matsaya guda daya a tsakanin kasa da kasa, da samar da wani matsayi na bai daya. Wang ya kuma yi kira da a mara baya ga zamowar Falasdinu cikakkiyar mamba a Majalisar Dinkin Duniya bisa amincewa da ita a matsayin kasar Falasdinu mai cin gashin kanta, da neman hanyoyin da za a bi don karfafa tabbatar da kafuwar kasashe biyu, da yin watsi da duk wani mataki na wani bangare guda da zai kawo cikas ga shawarar kafa kasashen biyu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp