A daren ranar 19 ga wannan wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump sun tattauna ta wayar tarho, inda shugaba Xi ya jaddada cewa, alakar Sin da Amurka na da matukar muhimmanci, Sin da Amurka na iya cimma nasarar bai daya da wadata tare, ta yadda za su amfani kawunansu, da ma sauran sassan duniya baki daya. A nasa bangare kuwa, shugaba Trump cewa ya yi, alakar Amurka da Sin ita ce mafi muhimmancin dangantaka a duniya, yana mai cewa, aiki tare tsakanin kasashen biyu ka iya haifar da manyan abubuwa da za su ingiza zaman lafiya da daidaito a duniya. Ya yi fatan wanzar da babbar dangantaka mai armashi ta dogon lokaci tsakanin kasarsa da Sin.
A cikin wannan tattaunawar, shugaba Xi ya bayyana ra’ayi da matsayin Sin kan batutuwan dake shafar dangantakar kasashen biyu, ya yi nuni da cewa, ya kamata Sin da Amurka su yi kokari da hadin gwiwa, kana kasar Amurka ta magance daukar matakan kayyade ciniki daga bangare daya, ta haka za a magance kawo illa ga nasarorin da kasashen biyu suka samu yayin shawarwarinsu a zagaye da dama. Game da batun TikTok, ana son ganin kamfanoni su tattauna bisa tushen ka’idojin kasuwanci, da cimma daidaito bisa dokokin kasar Sin da ka’idojin daidaiton samun moriya, ana fatan Amurka za ta samar da yanayin ciniki mai bude kofa da adalci da rashin nuna bambanci ga kamfanonin Sin da suka zuba jari a Amurka. Shugaba Trump ya bayyana cewa, Amurka tana fatan za a ingiza hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasashen biyu, kuma zai nuna goyon baya ga tawagogin kasashen biyu da su yi shawarwari don daidaita batun TikTok yadda ya kamata.
Akwai sharhin da aka yi game da cewa, tattaunawar dake tsakanin shugabannin kasashen biyu ta shaida cewa, Sin da Amurka sun samu muhimmin ci gaba kan cimma yarjejeniyar daidaita batun TikTok. Direktan ofishin nazarin siyasar kasa da kasa na kungiyar masana masu nazarin manufofin duniya na kwalejin ilmin zamantakewar al’ummar kasar Sin Zhao Hai ya yi fatan cewa, idan Sin da Amurka suka iya daidaita batun TikTok, to za a samar da sharadi ga kamfanonin kasashen biyu a kan yadda za su yi harkokin kasuwanci a kasuwar kasashen biyu, inda ta hakan za a sa kaimi ga Sin da Amurka wajen ganin sun daidaita sauran batutuwan tattalin arziki da cinikayya baki daya. (Zainab Zhang)