Dan wasan tsakiyar Barcelona Gavi zai yi jinyar watanni biyar bayan an yi masa tiyata a gwiwarsa, in ji kulob din a ranar Talata, likitoci sun yiwa Gavi aikin arthroscopy domin magance raunin da ya samu a gwuiwarsa ta kafar dama, an kiyasta lokacin dawowarshi kusan watanni 4-5, “in ji Barcelona a cikin wata sanarwa da ta fitar.
Dan wasan na Sifaniya mai shekaru 21 ya samu tsagewar mahadar kashi a shekarar 2023 a gwiwa, tun a watan Agusta Gavi bai taka leda ba, inda tun da farko Barcelona ta yi fatan maganin da aka dora shi akai zai magance matsalar, ba tare da bukatar yin tiyata ba.
Barca za ta ziyarci Real Oviedo ranar Alhamis a gasar La Liga kafin ta karbi bakuncin Real Sociedad a ranar Lahadi, sannan kuma za ta karbi bakuncin Paris Saint-Germain a mako mai zuwa a gasar zakarun Turai.
Gavi dai ba zai dawo ba sai a farkon shekarar 2026, shekarar da ake ganin kasar Sifaniya za ta kasance cikin kasashen da suka fi damar lashe gasar cin kofin duniya da za a buga a kasashen Amurka, Mexico da kuma Canada.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp