Daga ranar 19 zuwa 22 ga watan Satumba, 2025, dakarun sojojin Nijeriya sun kashe wasu ‘yan ta’adda, sun kama sama da mutane 20 da ake zargi da aikata laifuka, tare da ceto wasu da aka sace a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Sojojin sun kuma ƙwato makamai da dama ciki har da bindigogi ƙirar AK-47, bama-baman RPG, da harsashi sama da guda 700.
- Xi Ya Bukaci Hada Karfi Da Karfe Wajen Gina Yankin Xinjiang Ya Zama Mafi Kyau
- UNGA: Shettima Ya Tallata Damar Zuba Jari Na Dala Biliyan 200 A Fannin Makamashi A Nijeriya
Haka kuma sun ƙwato babura, kekuna, kakin soja, miyagun ƙwayoyi, motocci, da kuma man fetur da aka tace ba bisa ƙa’ida ba.
A Jihar Borno da wasu jihohin Arewa maso Gabas, sojojin sun daƙile hare-haren ISWAP/JAS, sun lalata bama-baman da aka dasa a kan hanya, tare da kama masu taimaka wa ‘yan ta’adda.
A wasu wurare kamar Sakkwato, Katsina, Taraba da Ribas, sojoji sun cafke masu garkuwa da mutane, sun lalata wuraren tace man fasa ƙwauri, tare da ƙwato kayayyakin sata.
Rundunar sojojin ta ce waɗannan hare-hare sun nuna ƙudirin gwamnati wajen yaƙi da rashin tsaro a faɗin ƙasar nan.
Ta kuma tabbatar wa ‘yan ƙasa cewa za ta ci gaba da ƙoƙari domin kare al’umma daga ‘yan ta’adda da sauran masu laifi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp