Babban Alkalin Kotun Majistare ta 1 dake Birnin Kebbi a Jihar Kebbi, Hassan Kwaido, ya daure wani Mubarak Lawali Kamba, shekaru biyu a gidan gyaran hali tare da yi masa bulala 40 bisa laifin tura hotunan batsa ga wata Farida Aliyu, matar wani Aliyu Abubakar.
Da mai kara (Farida Aliyu) da Wanda ake zargi (Mubarak Lawali) dukkansu mazauna garin Kamba ne dake karamar hukumar Dandi a jihar.
Da yake bayanin abin da ya faru a gaban alkalin kotun, dan sanda mai shigar da kara, Sufeto Jibril Abba, ya shaida wa kotun cewa lamarin ya faru ne a watan Yuli a garin Kamba kuma an kama Mubarak ne wanda ake zargi bayan da mijin Farida (Aliyu Abubakar)y kai karar ofishin ‘yan sanda.
Sufeto Abba take ya mika wa alkali nambar wayar salular Farida da Mubarak, nan take alkali ya tabbatar da ganin nambar wayar Mubarak acikin wayar salular Farida tare da ganin hotunan batsa a wayarta wadanda ya aike ma ta (Farida) da nufin yin lalata da ita.
Kwaido ya ce bayan ya gamsu da hujjojin, ya yanke wa Mubarak zaman gidan gyaran hali na tsawon shekaru biyu tare da bulala 40 sannan kuma zai biya tarar Naira dubu 50 da kuma wata karin Naira dubu 50,00 da za a bai wa Farida.