Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Engr. Rabiu Musa Kwankwaso ya gamu da fushin fusatattun matasa a jihar Kogi yayin da suka yi masa ihon “ba ma so” sabida ya fara ziyartar Bangaren NNPP masu biyayya ga Yarima Abubakar Audu.
An jefi Kwankwaso da ruwan leda a lokacin da ya kai ziyara a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, wanda ya ziyarci garin Ogbonicha, mahaifar marigayi Yarima Abubakar Audu, sannan ya koma Lokoja, inda wani bangare na jam’iyyar NNPP ya yi masa liyafar maraba, sai dai hakan bai wa magoya bayansa na babban birnin Kogi dadi ba, sun kalubalanci dan takarar da nuna kulawa ga bangaren Yarima Audu fiye da bangarensu (Lokoja).
Wasu daga cikin mambobin NNPP da suka zanta da manema labarai, sun koka da cewa tun da sanyin safiya a Lokoja, dan takarar shugaban kasan ya watsar da su yabi bayan magoya bayan yarima Audu wadanda suka ce har yanzu mambobin jam’iyyar APC ne.
Sai dai, Daily post Nigeria ta kara da cewa, Jami’an tsaro sun kaiwa dan takarar daukin gaggawa Inda suka garzaya dashi wani Shahararren otel dake Lokoja.
Wani mai taimaka wa Kwankwaso kan harkokin yada labarai, wanda ya bayyana kansa da suna, Musa Yunusa, ya bayyana abin da magoya bayan suka yi a matsayin al’ada ce a harkokin siyasa, inda ya ce, Kogi gida ce a wurin dan takarar shugaban kasa na NNPP.