Matatar Man Fetur ta Dangote ta sanar da cewa ta dawo sayar da fetur a kuɗin Naira.
Wannan mataki ya biyo bayan shiga tsakani na shugaban kwamitin sayar da fetur a kuɗin Naira ya yi.
- Bukatar Mutane Su Kula Da Warin Jikinsu
- Firaministan Sin: Adalci Shi Ne Abu Mafi Daraja A Wurin Kasashen Duniya
Yanzu ‘yan kasuwa za su iya sayan man fetur da biyan kuɗi a kuɗin Naira, ko dai su zo su ɗauka da kansu ko kuma a kawo musu a wuraren da aka amince da su a faɗin ƙasar.
A baya, matatar ta daina karɓar Naira wajen sayar da fetur saboda matsalolin da suka shafi canjin kuɗi da farashin ɗanyen mai.
Amma ƙoƙarin kwamitin da aka kafa domin ƙarfafa amfani da Naira wajen sayen ɗanyen mai da cinikayyar man fetur ya taimaka wajen warware matsalolin da ke tsakanin matatar da abokan cinikinsa, lamarin da ya sa aka dawo sayar da man da kuɗin Naira.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp