Ofishin jakadancin Sin a jamhuriyar Nijar, ya shirya liyafar murnar cika shekaru 76 da kafa jamhuriyar jama’ar Sin, da kuma maraba da sabon jakadan Sin a kasar Lv Guijun.
Liyafar ta ranar Juma’a 26 ga watan nan, ta samu mahalarta fiye da 400, ciki har da mukaddashin ministan harkokin wajen Nijar, kana ministan shari’a Alio Dauda, da ministan aikin gona Kanar Mahaman Elhadj Ousmane, da manyan jami’an gwamnati, kamar sakataren harkokin waje, da sakataren tsaro, da kwamandan ‘yan sandan kasa, da magajin garin Niamey. Sauran sun hada da mataimakin shugaban kwamitin tattauna batun sake ginin kasa, da jiga-jigan wakilan al’umma, da jakadun kasashen waje, da wakilan kungiyoyin kasa da kasa, da wakilan kamfanonin Sin, da shugabannin al’ummar Sin a Nijar da sauransu.
Cikin jawabinsa yayin liyafar, jakadan Lv ya waiwayi nasarorin da Sin ta samu cikin shekaru 76 da suka gabata, inda ya bayyana shawarar da Sin ta gabatar game da tsarin shugabancin duniya, ya kuma gabatar da sakamakon hadin gwiwa tsakanin Sin da Nijar a fannoni daban-daban. Ya ce ci gaban Sin mai zurfi, da kasuwar bai daya, sun samar da damammaki ga kasashen Afirka ciki har da Nijar.
Lv ya kara da cewa, matsayinsa na sabon jakadan Sin a Nijar, zai yi aiki tare da al’ummar kasar bisa yarjejeniyoyin shugabannin kasashen biyu, domin aiwatar da sakamakon taron kolin na Beijing, na dandalin tattauna hadin kan Sin da Afirka, da kuma kara fadada ma’anar dangantakar abota ta Sin da Nijar bisa manyan tsare-tsare. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp