Ma’aikatar sufuri ta kasar Sin, ta ce adadin zirga-zirgar fasinjoji yayin hutun bikin tsakiyar kaka na Sin dake tafe nan da ‘yan kwanaki, zai kai kimanin biliyan 2.36.
Da yake karin haske kan hakan, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Lahadin nan, mataimakin ministan ma’aikatar Li Yang, ya ce yayin kwanaki takwas na hutun da za a fara tun daga ranar Laraba, za a samu karuwar tafiye-tafiye na yawon bude ido ko na ziyartar ‘yan uwa.
Li, ya kara da cewa, an yi kiyasin ganin tafiye-tafiye kimanin miliyan 295 a duk rana cikin kwanakin hutun masu zuwa, karuwar da ta kai kaso 3.2 bisa dari kan na shekarar 2024 da ta shude.
An kuma yi hasashen kaso kusan 80 bisa dari na jimillar tafiye-tafiyen za a yi su ne ta amfani da ababen hawa masu zaman kansu. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














