A yau Lahadi ne aka gudanar da biki mai taken “Bude sabon babi a sabon zamani: Bikin zurfafa hadin gwiwa tsakanin CMG da bangarori daban daban na Macao” a yankin Macao na kasar Sin. Shugaban babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG Shen Haixiong, ya halarci bikin tare da gabatar da jawabi.
Cikin jawabin nasa, Shen Haixiong ya ce “A yau CMG ya sake kaddamar da ayyukan hadin gwiwa da dama tare da bangarori daban daban na Macao, kamar gabatar da wani fim mai bayana labarai mai suna “Macao: Gidan adana kayayyakin tarihi a fili”, da kuma fitar da “Gadon ruhin kishin kasa: Hanyar yawon shakatawa ta wuraren tarihi dake nuna kishin kasa na Macao”, ta yadda ya taimaka wa Macao wajen shiga tsarin samun ci gaban kasa.
Ya kara da cewa, CMG na fatan yin hadin gwiwa mai zurfi tare da gwamnatin yankin musamman na Macao, da abokai na bangarori daban daban, da kuma rubuta sabon babi game da gudanar da ayyukan dake shafar manufar “Kasa daya, mai tsarin mulki biyu” a Macao.
A dai yau din, an kuma gudanar da bikin kaddamar da shiri na musamman na “Sha’awar Xi Jinping ga al’adu”, da kuma shiri na musamman na “Bayanai kan jerin tunanin tattalin arziki na Xi Jinping” a yankin na Macao, wadanda CMG ya shirya su.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp