Ministan ma’aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin Yin Hejun, ya ziyarci helkwatar hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka ta AU, inda ya gana da kwamishinan AUn mai lura da harkokin ilimi, kimiyya da kirkire-kirkiren fasaha Gaspard Banyankimbona.
Yayin ganawar manyan jami’an a ranar Juma’a 26 ga watan nan, sun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, a madadin gwamnatin janhuriyar jama’ar kasar Sin da kungiyar AU, dangane da hadin gwiwar raya kimiyya da fasaha.
Wannan ce yarjejeniya tsakanin gwamnatoci ta 120 da Sin ta kulla, a fannin raya hadin gwiwar kimiyya da fasaha. Kuma karkashinta, sassan biyu za su yi hadin kai wajen aiwatar da bincike, da gina dandalin hadin gwiwa na raya fasahohi, da aiwatar da musayar kwarewar fasahohi, da kirkire-kirkire da sana’o’i, da goyon bayan musayar binciken kimiyya, da inganta hadin gwiwar kawance tsakanin sassan biyu, a daukacin bangarorin kimiyya da kirkire-kirkiren fasaha.
A tsokacin da ya gabatar yayin zaman, minista Yin Hejun, ya ce Sin na fatan yin aiki tare da kasashen Afirka, a fannin samar da tallafin fasahohi na gina al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya a sabon zamani a dukkanin sassa, ta hanyar aiwatar da yarjejeniyar ta hadin gwiwa.
A nasa bangare kuwa, Gaspard Banyankimbona, bayyana aniyar AU ya yi ta amincewa da yarjejeniyar da aka rattabawa hannu, wadda ya ce dama ce ta kara zurfafa hadin gwiwa na zahiri, a fannin kimiyya da fasaha tsakanin Sin da kasashen Afirka, da aiki tare wajen bayar da gudummawar bunkasa tattalin arziki, da zamantakewar al’umma, da walwalar al’ummun Sin da na Afirka. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp