Yau 29 ga wata, ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin(JKS) ya gudanar da taro don tattauna manyan batutuwa game da tsara shirin raya tattalin arziki da zaman al’umma na shekaru biyar biyar karo na 15. Babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping ne ya jagoranci taron.
Taron ya yanke shawarar cewa, za a kira cikakken zama na 4 na kwamitin kolin JKS karo na 20 daga raneku 20 zuwa 23 ga watan Oktoba mai zuwa a birnin Beijing.
Ofishin Siyasar ya saurari rahoton shawarwari da aka gabatar game da tsara shirin raya tattalin arziki da zaman al’umma na shekaru biyar biyar karo na 15. An yanke shawarar cewa, za a yi gyare-gyare ga daftarin shirin bisa tattaunawar da aka yi a taron da aka gudanar a yau, sannan za a gabatar da shi ga cikakken zaman don a duba shi.(Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp