Mai shari’a Emmanuel Danjuma Subilim na kotun masana’antu ta kasa (NIC) da ke Abuja, ya dakatar da kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Nijeriya (PENGASSAN) daga shirin tsunduma yajin aiki a kan matatar man Dangote.
Kotun, a wani hukunci da ta yanke a ranar Litinin, ta dakatar da wadanda ake kara da suka hada da kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL), hukumar dake kula da albarkatun man fetur ta kasa (NMDPR), daga katse danyen mai da iskar gas zuwa matatar Dangote.
- FCT Ta Amince Da Naira Miliyan 8.2 Kan Kujerar Aikin Hajjin 2026
- Za A Kira Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin Jam’Iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin Na 20
Wani babban Lauyan Nijeriya, George Ibrahim, wanda ke kare Dangote ne ya bayar da hujjar bukatar dakatar da waɗanda ake ƙara kan duk wani yunƙurin kawo cikas ga matatar ta Dangote.
A taƙaitaccen hukuncin da ya yanke kan ƙarar, Mai shari’a Subilim ya bayyana cewa, ci gaba da yajin aikin zai lalata kasuwancin matatar da gurgunta mafi mahimmancin ayyukan ci gaban tattalin arzikin al’ummar Nijeriya.
Alƙalin kotun ya ce, dokar hana ci gaba da yajin aikin za ta ci gaba da aiki har tsawon kwanaki bakwai ne kacal.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp