Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, sun sace fasinjoji da dama a kan hanyar Ibbi-Bussa, tsakanin Mokwa zuwa New Bussa, a Jihar Neja.
Cikin waɗanda aka sace akwai Ahmed Mohammed, Kwamishinan Hukumar Zaɓen Jihar Neja (NSIEC), da kuma Alhaji Bawa Niworo, tsohon Shugaban Hukumar Ilimi Ta Farko (SUBEB).
- Bam Ya Hallaka ‘Yan Sa-kai Biyu A Yobe
- ASUU Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwanaki 14 Don Biyan Buƙatunta
Shaidu sun ce ‘yan bindigar sun tare motocin fasinjoji da dama a kusa da dajin Ibbi a Ƙaramar Hukumar Mashegu da daddare a ranar Litinin, inda suka yi awon gaba da mutane da yawa.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun fara kai hari kan shingen binciken ‘yansanda a kan hanyar, inda jami’an suka mayar da martani.
A lokacin, sun yi wa motar ‘yansanda ruwan harsasai yayin da ɗaya daga cikin jami’an ya ji rauni, amma an garzaya da shi asibiti.
Ya ƙara da cewa daga baya ‘yan bindigar sun sake tare wata hanya a gaba, inda suka sace fasinjoji a motoci uku.
Abiodun, ya ce an tura ƙarin jami’an ‘yansanda tare da sauran jami’an tsaro da mafarauta don bin sahun ‘yan bindigar, da nufin ceto waɗanda aka sace da kuma cafke masu laifin.
A wani samame daban, Abiodun ya bayyana cewa rundunar ‘yansandan tare da mafarauta sun kai farmaki wani dajin da ake zargin maɓoyar masu garkuwa, a cikin dajin Kokolo da ke Ƙaramar Hukumar Magama.
A lokacin arangamar da aka yi da ‘yan bindigar, an kashe uku daga cikinsu, yayin da wasu suka tsere da raunuka.
An kuma ceto wani daga cikin waɗanda aka sace.