Abokai, a cikin shirin “Labaran Xinjiang a zane” a yau, za mu duba yanayin fannin ba da ilmi a jihar Xinjiang ta Sin.
A bana, iyalin Maitibake Tuersongmaiti,mazaunin kauyen Tuohula dake gundumar Hotan na Xinjiang, suna cikin farin ciki. “Yarona ya shiga makarantar midil, ya tafi wani wuri mai kyau a fannin muhallin rayuwa don karatu, saboda haka mun yi farin ciki sosai,” in ji Maitibake. Yana da ’ya’ya uku, babban dansa ya shiga makarantar midil ta goma ta birnin Karamay, dansa na biyu yana makarantar firamare a kauyensu, kana karamar cikinsu, ta shiga gidan renon kananan yara a watan Satumban da ya gabata. Ya ce, “Duk ’ya’yana uku suna zuwa makarantu a kusa da gida, kuma suna karatu a kyauta, yayin da yanayin makarantu ya fi na lokacinmu sosai.Malamansu dukkansu sun yi karatun jami’a.”
Sauye-sauyen da aka samu ta fuskar aikin ilimi a kauyen Buzhak na Hotan, misali ne na bunkasuwar aikin ba da ilmin tilas kyauta a Xinjiang.
Shekaru 70 da suka gabata, jami’a daya kacal da makarantun sakandare tara, da makarantun firamare 1,355 kacal jihar Xinjiang ke da su, kuma kashi 19.8% na yaran da suka isa shekarun makaranta ne kawai ke shiga makaranta, kana kashi 90% na mutanen yankin jahilai ne. Amma yanzu, a jihar Xinjiang, akwai makarantar kula da kananan yara daya ga duk yara 106, makarantar firamare daya ga duk yara 817, kuma kashi 97.74% na yaran sun shiga makarantar sakandare.
Yanzu a Xinjiang, mafi kyawun gine-gine su ne makarantu, kuma mafi kyawun wurin shakatawa shi ne harabar makaranta. Ci gaban da ake samu a Xinjiang wajen ba da ilimi yana ta samun ingantuwa, daga matsayin “samun makaranta” zuwa na “samun ingantaccen ilimi.” Bambance-bambancen ingancin aikin ilimi tsakanin yankuna, kauyuka da birane, da makarantu, suna raguwa bisa tallafin gwamnati da amfani da fasahar zamani, da ingantaccen rabon albarkatu. Karin iyalai kamar na Maitibake suna da kyakkyawar damar tabbatar da makoma mai haske, da cimma burikan da suka sanya, ta hanyar neman karin ilimi.(Mai zane da rubutu: MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp