Kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa ta yabawa gwamna Uba Sani bisa aiwatar da tsarin albashin ma’aikatan lafiya a jihar.
Hakan na na kunshe ne a cikin wata takarda da shugaban kungiyar na jihar, Ishaku Yakubu da sakatariya ta jihar, Christiana Bawa suka sanya wa hannu sannan suka mika wa gwamnan a ranar Talata.
Kungiyar ta bayyana matakin a matsayin wani gagarumin aiki na adalci da karamci, wanda ya dawo da kwarin gwiwar ma’aikatan jinya da ungozoma a gwamnatin jihar.
Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan aiki daya tilo na karamci da adalci ya sake farfado da fatan ma’aikatan jinya da yawa a cikin gwamnatin ku da kuma a cikin ajandar sabunta fata na Shugaban kasa,” in ji sanarwar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp