Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin JKS, sun halarci bikin girmama mazan jiya da da aka yi da safiyar yau Talata a dandalin Tian’anmen dake tsakiyar birnin Beijing, inda suka ajiye kwandunan furanni.
An gudanar da bikin ne albarkacin ranar tunawa da mazana jiya, rana guda gabanin ranar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin. A bana aka cika shekaru 80 da samun nasara a yakin da Sinawa suka yi da Japanawa masu kutse da yakin duniya na II.
Sauran shugabannin da suka halarci bikin sun hada da Li Qiang da Wang Huning da Cai Qi da Ding Xuexiang da Li Xi da kuma Han Zheng tare da wakilai daga dukkan bangarorin rayuwa na kasar Sin.
Da misalin karfe 10 na safiya dukkan mahalarta suka rera taken kasa, sai kuma shiru da aka yi na wani lokaci domin girmama wadanda suka sadaukar da rayukansu wajen ‘yantar da al’ummar Sinawa da ci gaban Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin.
An kuma ajiye manyan kwanduna 9 na furanni a gaban ginin tunawa da mazan jiyan.
Xi Jinping da sauran shugabannin sun yi tattaki zuwa gaban ginin, inda ya gyara furannin dake cikin kwandunan. Sannan ya zagaya ginin a wani mataki na nuna girmamawa. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp