Gwamnatin Jihar Gombe, ta sanar da wasu sabbin dokoki domin kauce wa rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya a yayin kakar girbin amfanin gona ta bana na shekarar 2025/2026.
Kwamishinan Harkokin Noma da Kiwo, kuma Shugaban Kwamitin Sulhunta Rikicin Manoma da Makiyaya, Dr. Barnabas M. Malle, ne ya bayyana matakan cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Litinin, 29 ga Satumba, 2025.
Ya ce sauran matakan da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da su sun haɗa da haramta shigowar makiyaya daga makwabtan jihohin daga watan Oktoban 2025, har zuwa Janairun 2026, da kuma takaita zirga-zirgar makiyaya tsakanin kananan hukumomin jihar, da ma tabbatar da dokar hana kiwo da dare daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 6 na safe.
Sauran matakan sun haɗa da haramta sayar da amfanin gona kafin makota su kammala girbi da hana girbi da fitar da amfanin gona da dare, kana ya da umarci manoma da makiyaya da su guji ɗaukar doka a hannunsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp