Kylian Mbappe ya zura kwallo uku rigis a wasan da Real Madrid ta doke Kairat Almaty ta kasar Kazakhstan a ranar Talata, inda kuma ya taka wani matsayi a tarihinsa na kwallon kafa yayinda ya cimma kwallaye 60 da ya zura a gasar zakarun Turai a kungiyoyin kwallon kqfa uku da ya bugawa gasar.
Kyaftin din na kasar Faransa ya zura kwallonsa ta farko a wasan a wani bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan golan Almaty Sherkhan Kalmurza ya buge Franco Mastantuono a cikin da’ira ta 18, ya kuma jefa kwallonsa ta biyu a minti na 52 bayan doguwar kwallon da Thibaut Courtois ya bugo, a minti na 67 ne Dani Ceballos ya yi wa Valeri Gromyko keta, inda aka ba Kairat bugun fanareti, amma an soke hukuncin bayan tantancewar VAR.
Arder Guler ne ya bayar da kwallo ta uku da Mbappe ya ci a wasan kafin Eduardo Camavinga da Brahim Diaz su zura kwallaye daya-daya kowanensu, kwallayen da Mbappe ya ci su ne na 58 da na 59 da kuma 60 a gasar zakarun Turai kuma hakan ya sa ya wuce tsohon dan wasan Bayern Munich Thomas Muller inda ya zama dan wasa na shida da ya fi zura kwallaye a tarihin gasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp