Ƙungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Nijeriya (PENGASSAN) ta dakatar da yajin aikin da ta fara a kan batun ma’aikatan Matatar Man Dangote, wanda kuma ya janyon ƙungiyar shiga yajin aiki a faɗin ƙasar nan.
Shugaban ƙungiyar, Festus Osifo, ne ya sanar da haka a Abuja a ranar Laraba.
- Kwamitin Shura Na Kano Ya Dakatar Da Malam Lawan Triumph Daga Yin Wa’azi
- Nijeriya Za Ta Fara Ɗaukar Mataki Kan ‘Yan Ƙasashen Ƙetare Da Bizarsu Ta Ƙare
Ya ce an dakatar da yajin aikin ne saboda girmama ƙoƙarin da jami’an gwamnatin tarayya suka yi na shiga tsakani.
Sai dai ya gargaɗi cewa ƙungiyar za ta koma yajin aikin nan take idan Matatar Dangote ta gaza cika sharuɗan yarjejeniyar da aka cimma.
Tun a ranar Litinin ɗin nan dai aka fara tattaunawa tsakanin ƙungiyar da Matatar Mai ta Dangote tare da jami’an gwamnati, amma a farko an kasa cimma matsaya sai da manyan jami’an gwamnati suka sake shiga wanda suka haɗa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Darakta-Janar na DSS, Ministan Ƙwadago, Ministan Kuɗi, da kuma manyan jami’an Ma’aikatar Man Fetur.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp