Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, ya yaba wa ‘yan Nijeriya kana bin da ya bayyana a matsayin masu hakuri da juriya, wadanda kuma suke cikin mawuyacin hali ta fuskar zamantakewa da bangaren tattalin arziki.
A sakonsa na ranar samun ‘yancin kai ga ‘yan Nijeriya, jagoran ‘yan adawar ya yi zargin cewa; APC mai mulki a halin yanzu, ta yi watsi da ‘yan Nijeriya tare da makomarsu.
- Manyan Jami’an Kasashen Afirka Suna Fatan Fadada Hadin Gwiwa Da Kasar Sin
- Xi Ya Taya Jami’ar Tianjin Murnar Cika Shekaru 130 Da Kafuwa
Atiku ya koka da yadda ‘yan Nijeriya ke fama da radadin matsalar rashin tsaro, karuwar karancin abinci. rashin aikin yi da kuma rashin sa da samun wani ci gaba ko sauyin da zai canja wa ‘yan kasar rayuwar, illa fargaba da rashin tabbas da ke karuwa sakamakon rashin kulawar gwamnatin ta APC.
“Abin takaici ne a ce, a kasar da take da dimbin arzikin yawan al’umma da dukiyoyi, amma an mayar da miliyoyin mutanenmu ‘yan gudun hijira da barace-barace a kasarsu, duk gwamnatin da ta san abin da take yi, ta kuma san hakkin al’ummar da take mulka, tana kula da jin dadi da kuma tsaron wannan al’umma tare da ba shi muhimmanci a kan komai.”
“Abin da muke fuskanta a halin yanzu shi ne, yadda gwamnati ta yi watsi da al’ummarta, yunwa na kashe ‘yan Nijeriya, ‘yan bindiga na kashe al’umma, amma duk da haka; Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da sauran jami’an gwamnatinsa, sun zura idanu, ba tare da daukar matakin da ya dace ba.”
Yayin da yake kira ga ‘yan kasa kan cewa, kada su karaya ko fitar da rai daga rabo, Atiku ya tunatar da ‘yan Nijeriya cewa; shekarar 2027, wata dama ce da za a iya amfani da ita wajen kawar da wannan mulki na zalunci, domin tabbatar da ganin gobenmu ta yi kyau.
“Babban kyawun demokuradiyya shi ne, ‘yancin samun damar kada kuri’a, duk wadanda ake zalunta; musamman mutanenmu a halin da ake ciki yanzu, za su samu damar kawar da wannan azzalumar gwamnati a zabe mai zuwa. Babu shakka, wannan shi ne ikon da babu wani dan takara da zai iya kwacewa daga al’umma,” in ji shi.
Atiku ya kara da cewa, a shekara 65; Nijeriya ta kasance kasa wadda ke cikin wani yanayi da ya yi kama da mai tafiya a cikin yimbu, sakamakon rashin shugabanci tsawon shekaru da dama da kuma almundahana da ta dabaibaye kasar.
Sai dai, ya bukaci ‘yan Nijeriya su ci gaba da kasancewa cikin kyakkyawan fata da kuma sa ran samun canji nagari a kowane irin lokaci, yana mai jaddada cewa; idan aka samu shugabanci nagari, kasar za ta iya canzawa daga yadda take zuwa wani yanayi mai ban sha’awa da ake iya gani tattare da wasu sauran kasashe.
Shugaban ‘yan adawar, ya kuma yi wa ‘yan Nijeriya kyakkyawan fatan murnar cika shekara 65 da samun ‘yancin kai, da kuma fatan samun zaman lafiya da dorewar tattalin arziki baki-daya
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp