A yau Jumma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga Grand Duke Guillaume na Luxembourg bisa hawa karagar mulki.
Xi ya yi nuni da cewa, tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Luxembourg a cikin shekaru fiye da 50 da suka gabata, a ko da yaushe suna mutunta juna tare da daukar junansu a matsayin daidai, da kafa wani abin koyi na cimma nasarori a tsakaninsu da samun moriyar juna a tsakanin kasashen masu mabambantan girma, tsari da kuma matakan ci gaba.
Kazalika, ya ce, a halin yanzu, kasashen Sin da Luxembourg sun samu kyakkyawan hadin gwiwa a fannonin karafa, kudi, harkokin jigila da dai sauransu. Yana mai cewa, “Hanyar siliki ta sufurin jiragen sama” ta Zhengzhou zuwa Luxembourg ta ba da gudummawa wajen samun kwanciyar hankali da gudanar da al’amuran masana’antu ba tare da tangarda ba a tsakanin Sin da Turai.
Xi ya kuma ce, ina mai da hankali sosai kan bunkasa dangantakar da ke tsakanin Sin da Luxembourg, kuma ina son yin aiki tare da Grand Duke Guillaume, don ci gaba da daukaka alakar Sin da Luxembourg zuwa wani sabon matsayi, da kawo karin moriya ga jama’ar kasashen biyu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp