Ƴar wasan gaba ta tawagar Super Falcons ta Nijeriya, Ifeoma Onumonu, ta sanar da yin ritaya daga buga ƙwallon kafa a ranar Asabar, ta hanyar wallafa saƙo a shafinta na Instagram.
Onumonu ta bayyana cewa lokacin ya yi da za ta rataye takalmanta, domin ba wa matasa masu tasowa dama su nuna bajintarsu a filin wasa. Sai dai ta ce ritayarta ba ta nufin cewa za ta bar harkokin ƙwallon ƙafa gaba ɗaya.
- An Biya Falcons Duk Kuɗin Alawus, Kyautar $100,000 Da Gidaje Ga Super Falcons
- Gwamna Aiyedatiwa Ya Bai wa Ƴar Super Falcons Tosin Demehin ₦30m Da Gida
A tsawon shekaru fiye da 20, Onumonu ta bar tarihi mai kyau a fagen ƙwallon ƙafa, inda ta samu nasarori da dama tare da Super Falcons, ciki har da buga gasar Kofin Duniya, da kuma lashe Kofin ƙasashen Afrika ta Mata (WAFCON) a watan Yuni 2024.
Onumonu mai shekaru 31, ta rubuta cewa:
“Cike godiya a zuciya, nake yin bankwana da taka leda a filin wasa.”
Kafin ta wakilci Nijeriya, Onumonu ta fara buga wasa ne da ƙungiyar ƴan ƙasa da shekaru 23 ta Amurka, kafin ta sauya ra’ayi zuwa ƙasarta ta asali.
A matakin ƙarshe na buga ƙwallonta, Onumonu ta taka leda a kulob ɗin Montpellier na ƙasar Faransa, kafin ta yanke shawarar yin ritaya.
Ta kuma bayyana cewa tana da niyyar ci gaba da aiki a fagen kwallon kafa, ko a matsayin mai horarwa ko kuma mai ba da shawara, inda ta ce:
“Zan yi amfani da ƙwarewar da Allah ya bani wajen taimaka wa ƙungiyoyin ƙwallon kafa a Nijeriya.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp