Assalamu alaikum. Malam a kaset din malam Jafar na ji ya halatta mace ta yi wa mata ‘yan’uwanta limanci, toh in Ramadan ya zo nakan tara mata na musu, da yake duk anguwan na dan fi su karatu, toh kusan anguwan ba malamin sunna ko daya, shi ne suke nema na ba su aya ko hadisi a kan hakan malam a taimaka min don Allah?
Wa alaikumus Salam. To ‘yar’uwa ina rokon Allah ya jikan malam Ja’afar, mu kuma ya kyautata namu karshen, ya halatta mace ta yiwa ‘yan’uwanta mata limanci, saboda abin da aka rawaito cewa: Nana A’sha da Ummu Salama –Allah ya kara musu yarda- sun yiwa wasu mata limanci, Nawawy yana cewa wannan hadisin Baihaky ya rawaito shi a Sunan din shi, hakan Shafi’i a Musnad dinsa da sanadi mai kyau, Almajmu’u (4/187).
- Tashar Samaniya Ta Sin: ‘Yan Sama Jannati Na Kumbon Shenzhou-14 Sun Fara Tattaki A Wajen Tashar
- 2023: Rashin Halartar Osibanjo, Lawan, Amaechi Ya Janyo Dakatar Da Zaman Sulhun APC
Haka nan an rawaito cewa Annabi (SAW) ya sanya wa Ummu-waraka ladani, sannan ya umarce ta da ta yi wa matan gidansu limanci, kamar yadda Abudawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 491, kuma Albani ya kyautata shi.
Bisa dalilan da suka gabata za ki iya yi wa matan unguwarku limanci, tun da kin fi su karatu, Annabi (SAW) yana cewa: “Wanda ya fi iya karatun alkur’ani shi ne zai yi limanci” Muslim 1078.
Idan za ki yi musu limanci za ki tsaya ne a tsakiyarsu in suna da yawa, in kuma ita kadaice sai ta tsaya a damarki.
Allah ne mafi sani.