A ranar 3 ga watan ne hukumar ciniki ta duniya (WTO) ta gudanar da taron shekara-shekara na majalisar kula da harkokin cinikayya karo na uku a birnin Geneva na kasar Switzerland. Kasar Sin ta yi amfani da wannan dama domin daidaita wannan batu, inda ta fallasa tare da sukar matakin “harajin ramuwa” na Amurka daga bangare guda da gitta kariyar cinikayya, inda ta yi nuni da cewa, matakan kakaba harajin da Amurka ta dauka sun haifar da illa ga harkokin cinikayyar duniya, kana ta bukaci Amurka ta mutunta ka’idojin WTO, tare da yin aiki da dukkan bangarori don karfafa gudanar da harkokin kasuwancin duniya cikin kwanciyar hankali ba tare da tangarda ba.
Membobi irinsu Indiya, Brazil, Masar da Pakistan sun yi tsokaci sosai game da bayanan da kasar ta gabatar, inda suka jaddada cewa, sashen gudanar da hidimomi wani muhimmin bangare ne na tsarin samar da kayayyaki a duniya da kuma makomar kasuwanci a duniya. Ya kamata dukkan bangarorin su kiyaye ruhin tuntubar juna da hadin gwiwa, da tabbatar da daidaito da fayyace ma’anar tsare-tsaren manufofi, tare da hada hannu wajen inganta ci gaban cinikayya a duniya cikin lumana ba tare da tangarda ba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp