Wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Fu Cong ya wakilci kasashe masu ra’ayoyi kusan iri daya wajen yin jawabi kan takunkumin da aka saka daga bangare daya, a gun kwamiti na uku na babban taron MDD cewa, a yayin da aka cika shekaru 80 da kafuwar MDD, tilas ne kasa da kasa su maida hankali da kara yin hadin gwiwa don kin amincewa da wannan takunkumi da ake kakabawa ba bisa doka ba.
Fu Cong ya bayyana cewa, a halin yanzu, ana samun ra’ayin bangare daya da ka’idar mai karfi ya samu fifiko a duniya, sannan ana samun takunkumin da aka saka daga bangare daya. Kasashe masu tasowa da jama’arsu suna fama da takunkumin, wanda ya saba wa daidaiton ikon mallakar kasa da ka’idojin hadin gwiwa, kana ya tsoma baki kan harkokin cikin gida na wasu kasashe, da saba wa ka’idojin yarjejeniyar kafuwar MDD, da ra’ayin bangarori daban daban da kuma dokokin kasa da kasa.
Fu Cong ya jaddada cewa, Sin tana maraba da sanarwar ministocin kasashen kungiyar G77 da kasar Sin ta shekarar 2025, inda ta jaddada cewa, takunkumin da aka saka wa kasashe masu tasowa daga bangare daya sun kawo illa ga bunkasar tattalin arziki da zamantakewar al’umma har ma da fahimtar juna a tsakanin kasa da kasa. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp