Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya musanta zargin da ake yi cewa ya ce tsohon Shugaban Ƙasa marigayi Muhammadu Buhari, yana da alaƙa da ƙungiyar ‘yan ta’adda ta Boko Haram.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ikechukwu Eze, ya fitar Jonathan, ya ce maganganunsa a wajen ƙaddamar da littafin tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor, wasu kafafen yaɗa labarai sun juya su ta yadda ba su dace da abin da ya faɗa ba.
- Kasar Sin Ta Soki Matakan Harajin Amurka “Na Ramuwa” A WTO
- Nijeriya Ta Samu Kwarin Gwiwar Zuwa Kofin Duniya
Idan za a tuna a wani rahoto da ke yawo a wasu kafofin yaɗa labarai an ambato Dr. Jonathan ya yi ikirarin cewa Boko Haram ta taɓa zaɓar marigayi Muhammadu Buhari, ya wakilcesu a tattaunawa da Gwamnatin Tarayya, lamarin da ke nufin yana da hannu a matsalar Boko Haram.
Sai dai a cewar tsohon shugaban ƙasar, bayaninsa a wajen bikin ya kasance ne cikin nazari mai zurfi kan ƙalubalen tsaro a Nijeriya, don nuni kan dabarar mugunta da ruɗu da Boko Haram ta riƙa amfani da su a shekarun farko.
Ya jaddada cewa manufarsa ita ce nuna yadda Boko Haram, bisa yaudara ke yawan ambaton sunayen manyan mutane masu mutunci don haifar da rikice-rikice da rabuwar kai ta siyasa da kuma ɓata wa gwamnati suna a idon jama’a.
Sanarwar ta buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da yadda aka sauya maganganun Dr. Jonathan, tare da nanata jajircewarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban dimokuraɗiyya.