Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jajanta wa iyalan marigayi dattijon jiha, Ambasada Muhammad Jabbi Maradun.
Marigayi Ambasada Jabbi ya rasu yana da shekaru 82 a duniya a Abuja ranar Asabar, bayan ya sha fama da rashin lafiya.
- Gwamna Lawal Ya Gwangwaje Kamfanin Sufurin Mota Na Zamfara Da Motoci 50
- Ko Kin San… Amfanin Sabaya Ga Mace?
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana Ambasada Muhammad Jabbi a matsayin dattijo mai kishin ƙasa wanda ya jajirce wajen ganin an samar da jihar Zamfara.
Sanarwar ta ƙara da cewa: “A cikin baƙin ciki muke alhinin rasuwar Ambasada Muhammad Jabbi Maradun, fitaccen dattijon jiha kuma ɗan jiharmu ta Zamfara na gaskiya.
“An haifi Jakada Jabbi ne a ranar 12 ga Nuwamba a shakrar 1943, a Ƙaramar Hukumar Maradun.
“Ambasada Maradun ya taba zama jakadan Nijeriya a ƙasar Tunisia daga 1999 zuwa 2003.
“Ya yi fice a yunƙurin samar da jihar Zamfara.
“Bayan kafuwar jihar Zamfara, Ambasada Jabbi ya shiga gwamnatin soja ta farko a ƙarƙashin Kanar Jibril Bala Yakubu, inda ya riƙe muƙamin kwamishinan Kasuwanci, Masana’antu da Yawon Buɗe Ido.
“Ayyukan sa na siyasa sun haɗa da jam’iyyun GNPP, NPN, da NRC, kuma ya kasance mai ruwa da tsaki a jam’iyyar PDP.
“Aikinsa na ƙarshe na aikin gwamnati shi ne kwamishinan gwamnatin tarayya mai kula da Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga na ‘Allocation and Fiscal Commission’, muƙamin da ya riƙe cikin gaskiya daga 2005 zuwa 2015.
“A madadin al’ummar jihar Zamfara, muna miƙa saƙon ta’aziyyarmu ga iyalan marigayin, masarautar da al’ummar ƙaramar hukumar Maradun bisa wannan babban rashi, Allah ya gafarta masa kurakuransa, Ya sa Aljanna ce makomar sa.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp