A ‘yan makonnin nan nan sunan Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya mamaye manyan kanun labarun kafafen yada labaraui daban-daban sakamakon dambarwar siyasar da ta kunno kai a Jam’iyyar PDP tun bayan da dan takarar shugaban kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya zabi Gwamna Okow ana Jihar Delta a matsayin wanda zai mara masa baya maimakon Wike mai samun goyon bayan wasu kusoshin PDP.
LEADERSHIP Hausa ta yi nazarin abubuwan da suke faruwa domin gano wai me ya sa ake ta rububin Wike a tsakanin PDP, APC, NNPP da LP wadanda ake ganin su ne manyan jam’iyyun da za su fafata a zaben 2023.
- Wasu Fusatattun Matasa Sun Afka Wa Tawagar Sanata Kwankwaso A Jihar Kogi
- Firaministan Pakistan Ya Gode Wa Sin Bisa Taimakon Da Ta Baiwa Kasarsa Wajen Yaki Da Ambaliyar Ruwa
Da farko dai Gwamna Nyesom Wike ne ya jagoranci tabbatar da jam’iyyar PDP ta fita daga dambarwar da ta fada sakamakon matsalar shugabanci a karkashin tsohon shugaban jam’iyyar Uche Secondus, har zuwa daukar nauyin babban taron jam’iyyar da yadda ya tsayu don ganin samun nasarar zaben shugabannin jam’iyyar na yanzu.
Ya kuma jagoranci samar da sulhu da fahimtar juna a tsakanin ‘yan jam’iyyar a jihohin kasar nan. Wadannan da ma wasu ayyukansa suka sanya ya zama wanji jigo mai fada a ji a cikin jam’iyyar PDP na yankin Kudu maso Kudu da ma Nijeriya baki daya.
Wadanna na daga cikin dalilan da suka sa ake ta rububinsa a daga dukkan bangarorin siyasa a wannan lokacin.
A tsawon shekaru Gwamna Wike ya tsayu wajen tattaro jama’arsa ta hanyoyi da dama musamman ‘yan Jam’iyyar PDP har suka amince da shugabancinsa a fagen siyasa, ya kuma tsayu wajen gudanar da ayyuykan cigaba da bunkasa kasa tun da ya hau karagar mulkin Jihar Ribas, ayyukan da ya gudanar sun taimnaka wajen sanya soyayarsa a zukatan al’umma jihar har abin ya yi tasiri zuwa wasu jihohin yankin kudu maso kudu da suka hada Akwa Ibom Kross Ribas, Edo da Delta.
Kaifin hankalinsa da iya mu’amala da jama’a ya sanya yana da kyakyawar hulda da takwarorinsa Gwamnanion yankin wanda hakan ya sa suke saurara masa a kan duk abin da ya taso a fagen siyasar yankin dama kasa baki daya.
A duk abin da ya taso yana sanya Jiharsa ta Ribas da Yankin Kudu maso Kudu a gaba wajen kare rayuka da dukiyar al’ummarsa a ‘yan shekarun da ya yi yana mulkin jihar.
Ana iya ganin haka karara a lokacin da ya jagoranci kwamitin jam’iyyar PDP a zaben da aka yi na gwamnan Jihar Edo inda aka yi wa Mista Godwin Obaseki taron dangi.
Ya karya lagon ‘yan adawa a yayin da ya jagoranci takwarorinsa na jihar Delta, Ifeanyi Okowa da Gwamnan Jihar Oyoi Seyi Makinde suka tsayu wajen ganin jam’iyyar PDP ta samu nasarar a zaben dama wasu zabukkan da aka yi a yankin, Irin wannna sadaukarwar da Wike yake yi wa harkokin siyasa ya sanya ya zama jagora mai hagen nesa a siyasar yankin kudu masu kudu abin kuma da ya sa ‘yan siyasa daga dukkan bangarori ke rububinsa don samunm tagomashin da zai iya kawo wa tafiyar siyasar su.
A kan haka ake ganin yadda Atiku na PDP, Tinubu na APC da Peter Obi na jam’iyyar LP suke zawarcinsa don ya amince ya shigo su yi tafiyar siyasar 2023 tare.
Haka kuma Wike ya tsayu wajen kafa magoya bayansa a sassa daban-daban na tattalinh arzikn Nijeriya da siyasar kasar nan musamman a jam’iyyar PDP, bayani ya nuna cewa, shi ne ya tabbatar da nada tsohon shugaban jam’iyyar.
Miista Secondos bayan da kotu ta sallami Ali Modu Sharif ya kuma yi tasiri a nada shugaban jam’iyyar na yanzu, Ayoichiya Ayu.
Tasirin Wike ya zarce jiharsa ta Ribas, yana daga cikin masu fada aji a yankin Kudu maso Kudu gaba daya, jihojin da suka hada da Akwa Ibom, Ribas, Kross Ribas, Bayelsa, Edo da jjihar Delta.
Kidididgar kuri’un da suka fito daga yankin kamar yadda kudin rajistar Hukumar Zabe ta INEC ya ya nuna, yankin Kudu maso Kudu ne ya zo na uku a masu yawa kuri’u a cikin yankuna kasar nan inda mutum Miliyan 15.2 suka rajista wannan gaggarumin kari ne na Miliyan 12.8 da aka samu a shekarun baya.
Wadannan kuri’un ne ‘yansiyasa ke rububin ganin sun zama nasu shi ya sa suke neman hadin kan Gwamna Wike a tafiyarsu.
Takaddama da rikicin da ke tsakanin Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike da dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kara daukar sabon salo duk kuwa da kokarin da shugabanin jam’iyyar ke yi na samar da sulhu da daidaito a tsakanin manyan ‘yan jam’iyyar da magoya bayansu masu tasiri.
Cikin manyan dalilan da rikicin ya ta’azzara sun hada da zabar Gwamnan Jihar Detla a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar da kuma bukatar da bangaren Wike suka sa a yi na sai dai a sauke shugaban jam’iyyar Sanata Iyorchia Ayu daga kujerarsa a zabo wani daga wani bangare na kasar nan don kowanne bangare ya samu wakilci a cikin tafiyar.
Bukatar neman sauke shugaban jam’iyyar ya taso ne tun bayan da Atiku ya samu nasarar zama dan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar PDP a matsayinsa na dan yankin Arewa to a cewar su bai kamata wani dan arewa kuma ya kasance shugaban jam’iyyar ba in har ana son samar da tsarin raba daidai.
Taron Landan
A wani mataki na bazata Tsohon Matimakin Shugaban kasa kuma dan Takara shugaba kasa na jami’iyyar PDP Alhaji Abubakar Atiku ya yi na haduwa da Wike tare da wasu gaggan ‘yan jam’iyyar a birnin Landan a ranar Alhamis na makon jiya don rarrashin Gwamna Wike, inda tun da farko ya hadu dan takarar jam’iyyar LP Mista Peter Obi, tare da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Duk da taron da suka yi na Landan da sauran ganawar da aka yi don samar da fahimtar juna, LEADERSHIP Hausa ta tabbatar da cewa Gwamna Wike ya ki amincewa da shirin daidaita su da ake yi, ya kuma bijiro da sabbin ka’idoji da bukatu da sai har an amince da su kafin ya bayar da ka bori ya hau.
Bayani ya nuna cewa, a wajen taron wanda ya samu halartar Gwamnoni kamar su Seyi Makinde na Jihar Oyo, Samuel Ortom na Jihar Benuwai da Okezie Ikpeazu na Jihar Abia, Wike ya bayyana musu cewa, ba zai saurari duk wani mataki na sulhu ba sai an cika masa sharuddan da ya bayar na sulhu.
Gwamnan ya kuma nuna rashin jin dadinsa a kan yadda Atiku ya matso da abokan gabarsa na siyasa kusa da shi, sun kuma hada da tsohon shugaban jam’iyyar na PDP Prince Uche Secondus.
tsige shugaban jam’iyyar Sanata Ayu daga mukaminsa. Majiyar ta kuma bayyana cewa, bayan wannan bukatar, Wike na neman a bashi hurumin zabar wanda zai maye gurbin Ayu a mastayin shugaban jam’iyyar, yana kuma neman a sanya hannu a yarjejeniyar cewa, Atiku za iyi wa’adin mulki daya ne kawai in ya samu nasarar lashe zaben 2023 yana kuma neman a bashi hurumin zabar shugabanin majalisar kasa da wasu Ministoci in har jam’iyyar ta samu nasarar lashe zaben 2023 da ma wasu bukatu da zai cigaba da bijirowa a kai-akai.”
“Atiku na neman goyon baya na kuma ya zagaye kansa da abokan gaba na na cikin Jihar Ribas na wajenta. Ba yana tare da Uche Secondus? Da Godwin Obaseki, Austin Opara, Celestine Omehia, Lee Maeba, dukkan su na yaki da ni kuma yana neman in goya masa baya.
“Za mu cigaba da sanya ka’idoji daya bayan daya har zuwa lokacin zabe, in har bai amince da wanda bayar ba a mastayin shugaban jam’iyyar ba to wani sabon takaddama ya taso kenan har sai an cika mana alkawarinmu, ba zan taba goya masa baya ba kuma yana tare da masu yaki da ni,” kamar yadda aka nakalto Wike yana cewa, bayan taron da suka yi a Landan.
Idan za a iya tunawa Gwamna Wike, na daya daga cikin wadanda suka jagoranci ganin an zabi Secondus a matsayin shugaban jam’iyyar bayan da kotu ta yi watsi da shugabancin Sanata Modu Sheriff shi ne kuma ya jagoranci tabbatar da shirin ganin an tsige shi daga ofis.
An yi imanin cewa, Gwamnan ya jagoranci cire Secondus ne a shekarar da ta gabata saboda hankoronsa na neman tikin takarar shugaban kasa na jam’iyyar, wanda bai samu nasara ba.
A Shirye Atiku Yake Na A Yi Sahihin Sulhu Bayani ya nuna cewa, Atiku da gaske yake yi na neman sulhu kuma yana matukar kokarinsa, amma Atiku da makusantarsa basu fahimci tanade-tanaden da Wike yake yi ba, “A matsayinsa na dan takarar shugabancin kasa kuma kwararre a harkar siyasa, ya shirya hada kai da al’umma daga dukkan bangarori don tafiya da kowa da kowa domin babbar fatansa shi ne na a samu nasarar zaben da ke gaba.”
Wani dan jam’iyyar PDP da ya nemi mu sakaya sunansa ya nemi a kai zuciya nesa don a samar da sahihin zaman lafiya, ya ce, ba zai yiwu ba haka kawai mutun ya yi watsi da mutanen da aka yi shekaru suna tare a dare daya, wasu suna tare fiye da shekara 30, wai don kawai wani dan jam’iyya ya nemi ka rabu da su.”
“Idan za ku iya tuna bayan kammala zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Wike ya yi rubutu a shafinsa na facebook inda ya bayyana cewa, zai goya wa duk wanda ya samu nasara a zaben da aka yi, ya yi alkawarin ba zai bar PDP ba.
Ya ce, ‘Za mu goya wa Atiku baya don samun nasarar zaben shugaban kasa a 2023, yanzu batu ne na kishin kasa a wai kishin kai ba” in ji majiyar ta mu.
Sai jama’a bas u san inda wannan mastayar take na a halin yanzu. Makinde, Ortom, Ikpeazu Sun Nuna Damuwarsu Bayani ya nuna cewa, Gwamnonin da suke bangaren Wike suna dari-dari da yadda Wike sulhu musamman ganin tsaurarawar zai iya shafar nasu zaben da ke a gabansu.
Misali Gwamna Ortom da Gwamna Ikpeazu suna takarar kujerar Majalisar Dattwa wanda za a gudanar da zaben nasu a ranar daya da na shugaban kasa.
“Sun samu kansu a cikin tsaka-mai-wuya a kan yadda za su raba zaben na su dana shugaban kasa in lokaci ya zo, gwamnonin na tunanin kilu za ta iya jawo musu da bau.
“Haka kuma Gwamna Makinde na takarar neman wa’adi na biyu, wanda kuma sakamakon zaben shugaban kasa zai iya shafar hakoronsa na neman ta zarce,” kamar yadda majiyar ta mu ta bayyana mana.
Wike Ya Gargadi Shugabannin Jami’yya PDP Na Jihar Ribas Su Guji Aiki Tare Da Makiyansa Kokarin da manema labarai suka yi na tataunawa da makusancin Wike kuma mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa daga yankin Kudu maso Kudu, Chif Dan Orbih, ya ci tura kuma ya ki amsa sakon kar ta kwana da wayar da aka yi masa.
Sai dai wani faifan bidiyon da ke yawo a kafafen sadarwa na zamani ya nuna Wike na barazana ga duk wani dan jam’iyyar a jihar Ribas da baya goya masa baya musanman masu hulda da makiyansa.
Ya kara da cewa, “Bari in yi muku bayanin abin da baku sani ba, a siyasa, a duk lokacin da ka yi ikirarin kana tare da mu amma kuma gobe muka ganka tare da abokan gabarmu, to za mu yi amfani da dukkan karfinmu wajen mukusheka, muna iya barin abokan gabanmu kai tsaye don yin maganinka.
“Saboda haka dukkan ku masu zuwa Abuja kuna ganawa da makiya na zan tabbatar da sai na gama da ku, ba zai yiwu ba ku zo jiharmu ku samu kwangila da kudade sannan ku koma Abuja ku cigaba da tattaunawa da makiyanmu Ayu Ya Ki Kiran Babnan Taron Kwamitin Gudanarwar Jam’iyya PDP Don tsira da mukaminsa, Shugaban jam’iyyar PDP, Ayoichiya Ayu ya kasa kiran taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar, in ji wani daya daga cikin manbobin kwamitin da ya nemi a sakaya sunansa.
Tun da farko an sanya za a gudanar da taron ne a ranar Laraba 10 ga wata da ranar Alhamis na watan Agusta amma daga baya aka dage taron ba tare da bayar da wani kwakwaran dalili ba.
Yanzu muna fiye da mako biyu da kiran taron har yanzu babu wani bayani daga jagororin taron na yaushe za a gudanar da taron a nan gaba, sai dai wasu na zargin ana ganin Wike na iya anmfani da taron wajen tabbatar da ganin an tsige shugaban jam’iyyar shi ya sa aka ki gudanar da taron.
Shekarau Ya Dawo Jam’iyyar PDP A halihn yanzu kuma, a ranar Litinin ne Tsonhin gwamnan Jihar Kani kuma Sanata mai wakiltar mazabbar Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau ya sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar PDP, wannan yana faruwa ne bayan da Shekarau ya yi zargin jam’iyyar NNPP ba ta yi musu aldalci ba kuma ma an yaudare su tare da cin amanarsa.