A ranar 5 ga watan Oktoba ne, karamin ofishin jakadancin kasar Sin da ke Legas, ya gudanar da bikin bunkasa al’adun gargajiya na bikin tsakiyar kaka. A jawabin da ta gabatar, karamar jakadiyar kasar Sin Yan Yuqing ta bayyana cewa, bikin tsakiyar kaka, a matsayin wani muhimmin biki na gargajiya na al’ummar kasar Sin, yana dauke da ma’anonin al’adu na sake haduwa da juna da nuna godiya, kuma ya kasance wata muhimmiyar alaka ta inganta mu’amalar al’adu da cudanyar jama’a a tsakanin Sin da Nijeriya.
Ta kara da cewa, muna son yin aiki tare da kamfanonin kasar Sin na ketare, da masana, da abokai daga kowane fanni na rayuwar al’umma a Nijeriya, don hada hannu wajen aiwatar da shirin bunkasa wayewar kai a duniya da shugaba Xi Jinping ya gabatar. Har ila yau, bisa fatan sake haduwa a lokacin bikin tsakiyar kaka, za mu gina wata gada ta raya zumunci, da ci gaba da kyautata amincewa, da abokantaka, da karfafa fahimtar juna a tsakanin al’ummomi masu mabambantan wayewar kai, da kuma hada hannu wajen rubuta sabon babi na hadin gwiwa tsakanin Sin da Nijeriya.
Bugu da kari, Madam Yan ta bayyana a cikin wata hira da ta yi da gidan talabijin na Legas cewa, bana shekara ce ta cika shekaru 54 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Nijeriya, da kuma cika shekaru 25 da kafuwar dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. A shirye muke mu hada hannu da Nijeriya don gina al’ummar Sin da Nijeriya mai kyakkyawar makoma ta bai-daya a matakin koli. (Abdulrazaq Yahuza Jere)