Bisa gayyatarsa da jam’iyyar ‘yan kwadago ta kasar Korea ta Arewa (WPK) da gwamnatin Korea ta Arewar suka yi masa, firaministan kasar Sin Li Qiang, zai halarci bikin cika shekaru 80 na jam’iyyar WPK da kuma ziyarar sada zumunta a kasar, daga ranar 9 zuwa 11 ga wata.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ne ya sanar hakan a yau Talata, inda ya ce, kasashen Sin da Korea ta Arewa abokai ne kuma makwabta, kana rayawa da karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, muhimmiyar manufa ce ta JKS da gwamnatin kasar.
Ya ce, yayin da ake cika shekaru 80 da kafa jam’iyyar WPK, a shirye Sin take ta hada hannu da Korea ta Arewa karkashin wannan ziyara, domin bin jagorancin muhimmiyar matsaya da fahimtar dake tsakanin shugabannin jam’iyyun da kasashen 2, da karfafa tuntubar juna da musaya da hadin gwiwa da kuma daukaka dadaddiyar abotarsu da huldar hadin gwiwa. (Fa’iza Mustapha)