Ƙungiyoyin ma’aikatan jami’o’i na SSANU da NASU, ƙarƙashin kwamitin haɗin gwuiwa (JAC), sun gudanar da zanga-zanga a Abuja don neman gwamnatin tarayya ta cika alƙawarin yarjejeniyoyin da aka cimma tun 2022. Zanga-zangar ta gudana a Jami’ar Yakubu Gowon (tsohuwar Jami’ar Abuja) tare da makamanciyarta a wasu jami’o’i a faɗin ƙasar.
Shugabannin ƙungiyoyin, Comrade Nurudeen Yusuf da Comrade Sadiya Ibrahim Hassan, sun zargi gwamnati da sakaci da karya Alƙawurra. Sun ce gwamnati ta gaza aiwatar da sabunta yarjejeniyar 2009, biyan ƙarin albashi na 25% da 35%, da kuɗaɗen alawus na ₦50 biliyan da aka raba ba bisa ƙa’ida ba.
- Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo
- Alaafin Ya Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Kama Masu Kashe Kashe A Kwara
Ƙungiyoyin sun kuma koka kan ƙin biyan watanni biyu na albashi da aka riƙe musu, da rashin miƙa kuɗaɗen ake cire musu. Sun ce duk gargaɗin da suka yi bai haifar da sakamako ba, kuma sun gaji da kafa kwamitoci marasa amfani.
Shugaban NASU, Dr. Makolo Hasan, ya gargaɗi gwamnati cewa wannan zanga-zanga gargaɗi ce ta farko, kuma idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, ƙungiyoyin za su tafi yajin aiki gaba ɗaya.