Hukumar Rajistar Malamai ta Nijeriya (TRCN) ta nuna damuwa kan yawaitar malaman da ba su cancanta ba a kasar, inda ta bayyana hakan a matsayin babban dalilin raguwar ingancin ilimi.
Babban Daraktan TRCN, Dr. Ronke Soyombo ce ta bayyana hakan a ranar Litinin yayin bayyanarta a shirin ‘The Morning Brief na tashar Channels Telebision, a lokacin bikin Ranar Malamai ta Duniya ta 2025, mai taken “Sake Tsara Koyarwa a Matsayin Sana’a ta Hadin Kai.”
Dr. Soyombo ta yi bakin ciki da cewa mutane da yawa da ke koyarwa a makarantu a fadin Nijeriya ba su da cancantar da ake bukata don gudanar da aikinsu yadda ya kamata, abin da ya fi shafar makarantu masu zaman kansu.
“Akwai da yawa malamai marasa cancanta a cikin aikin. Muna da wadanda ke koyarwa a ajujuwa amma ba su da takardun shaidar koyarwa, musamman a makarantu masu zaman kansu,” in ji ta.
Ta bayyana cewa, yayin da wasu mutane ke da sha’awar koyarwa da gaske, rashin horo na hukuma ya hana su shiga aikin koyarwa.
Dr. Soyombo ta bayyana cewa TRCN a halin yanzu na da malamai masu rijista kusan miliyan 1.4, tare da shirin kara wannan adadi zuwa miliyan 20 cikin shekaru biyu masu zuwa ta hanyar dijital da saurin rajista.
“Mun zamanantar da tsarinmu domin mutane da yawa su sami damar yin rijista,” in ji ta. “Kowane malami yana da bai wa ta musamman wadda ta bambanta da ta wani. Amma abin da muke kokarin yi domin inganta ilimi shi ne kowa ya zo tare da tsarinsa na darussa.”
“Za ku iya zama malamai uku da ke koyarwa ga rukuni guda na dalibai, kuma idan kuka zo tsara darusa tare tabbas za ku samar da wani abu mai dimbin fa’ida fiye da lokacin da kake aiki kai kadai.”
“Babu shakka akwai karancin malamai, don haka abin da muke yi tare da wannan gwamnati shi ne gaggauta shirin Diploma na Kwarewa a Fannin Ilimi (PDE). Ga wadanda ba su da shi, yanzu lokaci ne da za su iya samun dama. Muna gaggauta kwas din zuwa watanni shida ga malamai masu kwarewa, domin da zaran sun kammala, za su sami kwarewa. Wannan zai sa mu samu isassun ma’aikata a fannin koyarwa.”
“Abin da TRCN ke yi kuma shi ne duba yadda za mu inganta malamai. Haka kuma, muna tallafa musu da kayan aiki a cikin ajujuwa, domin wasu malamai suna da kwarewa sosai kuma suna neman yadda za su tsara darussa don tallafawa sauran malamai, kuma hakan zai karfafa wasu su shigo,” in ji ta.
A halin da ake ciki, Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, a cikin sakonta na Ranar Malamai ta Duniya, ta yaba wa malamai kan gudummawar da ba za a iya misaltawa ba wajen gina kasa, sannan ta yi kira ga kokari na musamman don magance karancin malamai a duniya.
Tinubu ta bayyana malamai a matsayin “jarumai, masu tsara tunani, da jagorantar karni,” inda ya jaddada cewa inganta walwalarsu da ci gaban kwarewarsu na aiki shi ne mabudin karfafa tsarin ilimi.