Gwamnatin Jihar Bauchi ta cimma yarjejeniyar alƙawarin zuba jarin fiye da dala biliyan 5.2 bayan kammala Taron Tattalin Arziki da Zuba Jari na Bauchi, inda gwamnatin ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyi (MoUs) guda 47 tare da masu zuba jari daga cikin gida da ƙasashen waje.
Taron, wanda aka gudanar a sabon ɗakin taro na Sir Ahmadu Bello International Conference Centre, ya samu halartar ƴan kasuwa daga ƙasashen China, da Saudi Arabia, da Turkiyya, da Masar, da sauran ƙasashen, tare da fitattun ƴan kasuwa na cikin gida.
Shugaban kwamitin shirya taron, Farfesa Murtala Sabo Sagagi, ya bayyana cewa yarjejeniyoyin sun shafi muhimman fannoni kamar noma, da ma’adanai, da makamashi, da gine-gine, da masana’antu, da fasahar sadarwa (ICT). Ya ce daya daga cikin yarjejeniyoyin ya riga ya samar da zuba jari na dala biliyan 1 don bunƙasa masana’antar siminti da ayyukan gine-gine a jihar. Haka kuma, Bauchi ta ƙulla yarjejeniya da China Fuhai Energy Group kan aikin Petrochemical City Complex mai darajar dala biliyan 2.7.
- Wata Mata Ta Ƙona Al’aurar Ƙaramar Yarinya A Bauchi
- Wata Mata Ta Ƙona Al’aurar Ƙaramar Yarinya A Bauchi
Haka nan, African Athlete Academy ta yi alƙawarin zuba jari na dala biliyan 1 don gina cibiyar horar da matasa da wasanni ta zamani a jihar. Farfesa Sagagi ya ce taron ya kasance dandali na haɗin gwuiwa tsakanin gwamnati, masu zuba jari, da ƙungiyoyin farar hula, da abokan cigaba don amfana da damar tattalin arziƙin jihar Bauchi ta fuskar noma, da yawon bude ido, da ma’adanai.
A yayin rufe taron, Gwamna Bala Mohammed ya gode wa mahalarta bisa amincewarsu da zuba jari a Bauchi. Ya bayyana taron a matsayin ɗaya daga cikin mafi nasara a tarihin Nijeriya, tare da jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da samar da ingantattun hanyoyi, da gaskiya da riƙon amana a mulki, da kuma manufofin da ke ƙarfafa zuba jari a jihar.