Amurka da China da Rasha ba su cika haduwa a teburi daya ba, duk da cewa akwai wasu abubuwan da dama da suke haduwa a kai.
Dukkansu sun amince nahiyar Afirka ta samu kujerar dindindin a kwamitin tsaro. Amma shin me ya sa har yanzu ba a tabbatar ba?
A kwamitin tsaro na MDD, akwai kasashe biyar masu kujerar dindindin wato China da Rasha da Faransa da Birtaniya da Amurka, wadanda ake kira da P5. Su kadai ne mambobin da suke da damar hawa kujerar na-ki.
Sauran kasashen Majalisar Dinkin Duniya suna samun damar zama a kwamitin tsaron ne lokaci bayan lokaci, amma ba su da karfin ikon hawa kujerar na-ki.
‘Tabbatar da tsaron Afirka dole ne’
Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce akwai bukatar gyara.
“Ba za a taba yi iya samar da tsaro a duniya ba, ba tare da tabbatar da tsaron Afirka ba,” in ji shi.
“Bai dace ba a ce kwamitin tsaro na duniya babu wakilcin nahiyar da ke da sama da mutum biliyan 1, wadda kuma mutanenta ke kara hayayyafa, kuma yanzu haka nahiyar ce ke da kashi 28 na kasashen Majalisar Dinkin Duniya.”
Kungiyar Tarayyar Afirka ta bukaci “akalla kujera biyu ta dindindin” da karfin ikon hawa kujerar na-ki, da kuma karin kujera biyar da ba na dindindin ba.
Amma duk da cewa yawancin kasashen majalisar sun amince akwai bukatar Afirka ta samu damar, masanin diflomasiyya a majalisar, Richard Gowan ya ce ya ce ba su shirya ba.
Gowan ya ce gwamnatin Amurka a karkashin Biden ta bayyana goyon bayanta kan yunkurin Afirka na samun kujera biyu, amma ba tare da karfin kujerar na-ki ba. Amma ya ce Trump ya nuna cewa ya fi son kwamitin a yadda yake, kuma ba ya so kasashe masu karfin hawa kujerar na-ki su yi yawa.
Wadanne kasashe daga Afirka?
Wata babbar matsalar da ke ci wa Afirka tuwo a kwarya ita ce shin wace kasa ce ta fi cancantar darewa kujerar guda daya ko biyu a kwamitin?
Kasashen da ake bayyanawa daga Afirka su ne Afirka ta Kudu da Nijeriya da Kenya da Habasha da Algeriya da Masar, amma har yanzu babu kasar da ta fi shigewa gaba wajen nema.
Tarayyar Afirka na da mambobi 55, kuma ana tunanin kungiyar ta zama wakiliyar nahiyar, amma Gowan ya ce kungiyar tana fama da cikas wajen aikin diflomaiyya.
Ya ce ana samun matsaloli da dama wajen daukar mataki a kungiyar, “misali kan matsalar da ta shafi Somalia,” in ji shi.
“Masana diflomasiyya dan Afirka da ke New York suna tunanin ya fi dacewa su rika daukar matakai daban da na takwarorinsu na Tarayyar Afirka saboda suna tunanin China da Amurka ba za su goyi bayan abin da kungiyar ke so ba.”
A yanzu da aka taru a birnin New York domin taron na Majalisar Dinkin Duniya, abin jira a gani shi ne shin Afirka za ta samu kujerar ta dindindin ko kuma kawai za a ci gaba da tafka muhawara ne.