Ministan ma’adanai da samar da ci gaba, Dr. Dele Alake ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya kan tabbatar da ci gaba da yin gyare-gyaren da ake yi, inda ya bayyana cewa babu wata barazana ko ɓatanci da za ta kawo cikas ga ajandar kawo sauyin, wanda tuni aka fara samun sakamako mai kyau.
Dr. Alake ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen mako gabanin makon hakar ma’adinai na Nijeriya karo na 10, wanda zai fara a ranar Litinin 13 ga Oktoba, 2015.
- Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano
- Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya
A wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Segun Tomori, ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, ministan ya jaddada cewa, sauye-sauyen sun fara haifar da “ɗa mai ido”, kamar yadda alamu daban-daban suka nuna, ciki har da wadanda hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta tattara.
“Shekaru goma da suka wuce, gudummawar da ma’adanai ke bayarwa ga GDP na kasarmu bai wuce 0.5% ba, amma a yau ya karu zuwa 1.8% – alkalumman NBS suka nuna a cikin rabi na biyu na 2025 wanda ba a taba ganin irinsa ba”.
Da yake tsokaci kan ci gaban fannin, Ministan ya bayyana cewa, makon hako ma’adanai na Nijeriya ya yi nuni da yadda masana’antar ke sauya tunani zuwa tsari mai kyau, da sabbin abubuwa, da ke lalubo masu zuba jari na kasa da kasa.
Ya bayyana cewa, sauye-sauyen sun tattara ne a kan gaskiya, rage haɗari, da inganta masana’antar.