Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu ma’aurata da wasu mutane biyar bisa zarginsu da gudanar da ɗaurin aure ba tare da izinin iyayensu ba ko kuma bin tsarin addinin Musulunci a unguwar Nasarawa da ke cikin birnin Kano.
Wadanda ake zargin sun hada da ango mai suna Aminu mai shekaru 23 da amaryarsa Sadiya mai shekaru 22. Sauran wadanda aka kama su ne Umar mai shekaru 24 wanda ya kasance wakilin ango; Abubakar, mai shekaru 23, wanda ya kasance waliyyin amarya; Usaina, mai shekaru 21; da kuma wasu ‘yan mata guda biyu wadanda suka kasance shaidu a yayin ɗaurin auren.
- Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano
- Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya
Rahotanni sun bayyana cewa, an ɗaura auren ne akan sadaki Naira 10,000, ba tare da amincewar iyayen ma’auratan ba.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mataimakin babban kwamandan hukumar ta Hisbah, Dr. Mujaheeddeen Aminuddeen, ya ce an kama wadanda ake zargin ne biyo bayan korafe-korafen da ‘yan unguwar suka kai wa hukumar.
Ya bayyana cewa, matakin da wadanda ake zargin suka ɗauka ya saɓawa koyarwar addinin Musulunci da kuma dokokin aure na jihar, yana mai jaddada cewa, hukumar ta Hisbah ba za ta amince da duk wani abu da ya saɓawa tsarin addini da na shari’a a jihar Kano ba.
Dr. Aminudeen ya kara da cewa, a halin yanzu wadanda aka kama suna hannun Hisbah domin ci gaba da bincike.