Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya caccaki matakin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta dauka na fara yajin aiki na tsawon makonni biyu, yana mai bayyana matakin a matsayin wanda bai kamata ba kuma bai dace ba ganin irin kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na biyan kusan dukkanin bukatun kungiyar.
Da yake magana a wani shiri na gidan Talabijin na Channels, ‘The Morning Brief’ a ranar Litinin, Alausa ya bayyana rashin jin dadinsa da matakin da ASUU ta dauka na tsunduma yajin aiki duk da kokarin da gwamnatin ke yi akansu.
“A cikin shekaru biyun da suka gabata, babu wani batun yajin aikin ASUU, saboda kokarin da gwamnati ke yi akan biyan duk bukatunsu.
“A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, ni da mataimakin shugaban kwamitin tattaunawa na gwamnatin tarayya, mun tattauna da ASUU, zan iya gaya muku a yau, a zahiri, an biya kusan dukkan bukatun ASUU, don haka ban ga dalilin da ya sa ASUU ta fara yajin aikin ba.” In ji Ministan